Hukumar Kwastam ta Rasa Jami’inta Sanadiyyar Hatsarin Jirgin Ruwa
Wani jami’in hukumar Kwastam mai suna Aliyu AA ya riga mu gidan gaskiya a Legas.
Mai magana da yawun hukumar Kwastam, Idaho Sulaiman ya bada sanarwar rasuwar.
Sulaiman ya ce Aliyu AA ya rasu ne sakamakon hatsarin jirgin ruwa yayin da suka fita aiki Hukumar Yaki da Masu Fasabkwabri, Kwastam, Western Marine Command, WMC, a ranar Laraba ta ce ta rasa daya daga cikin jami’anta sakamakon hatsarin jirgin ruwa a ranar Litinin, rahoton The Nation.
Kakakin hukumar, Idaho Sulaiman ne ya sanar da hakan cikin sanarwar da ya fitar a Legas.
Read Also:
Ya ce lamarin ya faru ne misalin karfe 6.10 na yammacin ranar 22 ga watan Maris yayin da jami’an hukumar na yankin Akere karkashin Idiroko suka fita sintiri bayan samun bayannan sirri a yankin Vawhe-Isalu.
Suleiman ya ce tawagar karkashin jagorancin Sufeta na Kwastam, Ajayi AS, ta yi hatsarin ne yayin kokarin tare wani jirgin ruwa da ake zargin yana dauke da haramtattun kaya.
“Hatsarin ya yi sanadin rasuwar Mataimakin Sufeta na Kwastam, (AIC) Aliyu AA bayan nutsewa da ya yi a cikin ruwa.
“An gano gawar mamacin a kasan rafin da taimakon mazauna kauyen da ke kusa da ruwan yankin.
“An kai gawar zuwa babban asibitin Badagry daga bisani aka ajiye a dakin gawarwaki bayan likitoci sun tabbatar ya mutu.
“An dauki gawar a jirgin sama na MAX air zuwa Kano a ranar 23 ga watan Maris bisa umurnin yan uwan mamacin,” in ji shi.