Sojojin Sudan sun ƙwato Filin Jirgin Saman Khartoum Daga Hannun Dakarun RSF
Sojojin Sudan sun ƙwace iko gaba ɗaya da filin jirgin sama na babban birnin ƙasar, Khartoum daga hannun dakarun RSF da suka kwashe kusan shekaru biyu suna iko da shi.
Read Also:
Wasu daga cikin fararen hula sun riƙa hawa tituna suna murna da farinciki.
Dakarun na RSF sun riƙa janyewa daga yankunan da suke iko da su na birnin.
Sai dai har yanzu su ne ke riƙe da ikon yanwancin yankin Dafur, inda wasu shaidun gani da ido suka ce a farkon wannan makon gomman fararen hula ne hare-hare ta sama ya kashe a wata kasuwa.