Lai Mohammmed ya yi Martani Akan ‘Yan Ta’adda

 

Muna bukatar taimakon kasashen ketare don kawo karshen ta’addanci, cewar ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed.

A cewarsa, akwai makamai na musamman da ya kamata Najeriya ta mallaka, idan ba haka ba, ‘yan ta’adda za su cigaba da cutar da mutane.

Ministan ya fadi hakan ne lokacin da ya kai ziyara ga gwamnan Makurdi, Samuel Ortom, har yace akwai masu daukar nauyin ‘yan ta’addan.

Ministan Labarai da al’adu, Lai Mohammed, a ranar Litinin yace a yanzu haka an bar Najeriya da ‘yan ta’adda saboda an hana ta makaman yakar ‘yan ta’adda duk da kokarin da takeyi wurin yakarsu.

Ministan ya nuna alhininsa a kan kisan manoma 43 na Zabarmari, karamar hukumar Jere da ke jihar Borno, inda yace gwamnatin tarayya ba za ta zauna ba har sai ta kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Alhaji Mohammed ya yi maganar ne a Makurdi yayin da ya kaiwa gwamna Samuel Ortom ziyara, inda yace ‘yan ta’addan suna samun kudade daga kasashen ketare, Vanguard ta wallafa.

A cewarsa, “Idan mutane suna batun ta’addanci, basa ganin cewa zai iya addabar duniya gabadaya, sannan kowacce kasa tana fuskantar nata ta’addancin.

“Ba za mu dakata ba a kan kulawa da lafiya da walwalar al’umma ba, amma ya kamata jama’a su san cewa akwai masu daukar nauyin namu ‘yan ta’addan kuma muna bukatar kasashen duniya su tallafa mana.

“Misali, Najeriya tana bukatar makamai masu inganci wurin yakar ta’addanci amma ya ci tura, kuma idan ba mu da isassun makamai ‘yan ta’adda za su cigaba da addabarmu.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here