Lai Mohammed: Majalisa na Tuhumar sa a Kan N19m
Bayan Lai Mohammed ya gabatar da kasafin ma’aikatarsa na 2021 ne hukumar kididdiga ta fara yi masa tambayoyi na kure.
Ta ce ya aka yi ta ga yayi amfani da naira miliyan 19 lokacin kulle wanda aka ware musamman don tafiye-tafiyen kasashen ketare.
Ya amsa da cewa, sun yi amfani da kudaden ne kafin kullen COVID-19, wurin zuwa kasashe kamar Ingila da Spain don halartar taro daban-daban A jiya ne Ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed yayi bayani a kan kashe naira miliyan 19 wurin tafiye-tafiye lokacin kullen COVID-19.
Ya sha ‘yar kure a lokacin da ya je gaban kwamitin gabatar da kasafin ma’aikatarsa na 2021, Daily trust ta ruwaito. Wani mamba na kwamitin kasafi, Ezenwa Onyewuchi ya ce masa:
Read Also:
“Bari in tuna maka abubuwan da kace a kan kasafin 2020. An baka naira miliyan 30 don tafiye-tafiye cikin kasa, kace ka kashe naira miliyan 23, an baka naira miliyan 96, ka kashe naira miliyan 90.
“Batun tafiye-tafiyen kasashen ketare, an baka miliyan 43, ka kashe miliyan 19. Ina mamakin yadda ka iya fita kasashen ketare a lokacin kulle, wanda aka hana kowa fita kasashen waje, har da za kace ka kashe naira miliyan 19.
” Ministan ya amsa wannan tuhumar da cewa ya kashe naira miliyan 19 ne a tafiye-tafiyen kafin a kulle kasashe saboda COVID-19.
“Idan ka lura an yi kasafin naira miliyan 43 ne, amma kasa da kashi 40 bisa darin kudin muka kashe, saboda mun je taro daban-daban a kasashen ketare, tun daga taron UNWTO, UNESCO da aka yi a Spain da kuma Ingila. Mun yi wani taron na daban a Ingila duk kafin a kulle kasashe.
“Ina tunanin tafiyar da muka yi ta karshe ita ce wacce muka je Addis Ababa, inda muka raka shugaban kasa taron AU a wuraren watan Maris 2020 kafin kullen. “Idan za ku tuna, karshen watan Maris ne akayi kullennan. Don haka duk abubuwan da muka kashe kafin kulle ne,” Lai ya ce.