Matsalar Tsaro: Gwamna Lalong ya ja Kunnen Shugabannin Karamar Hukumar Jos ta Arewa

 

Gwamnan jahar Filato, Simon Lalong, ya ja kunnen shugabannin karamar hukumar Jos ta arewa.

Ya ce su yi gaggawar kawo karshen ta’addancin da ke aukuwa a bangarensu don gwamnati ba za ta ci gaba da lamuntar hakan ba.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a ranar Litinin da daddare yayin wani taro da suka yi a gidan gwamnati da ke Rayfield a Jos.

Jos, Filato – Gwamnan jahar Filato, Simon Bako Lalong, ya ja kunnen shugabannin karamar hukumar Jos ta arewa a kan su yi gaggawar kawo karshen rikici da ta’addancin yankin.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a ranar Litinin ta dare yayin wani taro a gidan gwamnati da ke Rayfield, Jos tare da masu ruwa da tsakin yankin a matsayin hanyar kawo zaman lafiya a yankin, Daily Trust ta rawaito.

Daily Trust ta rawaito cewa, ya yi jan kunnen ne bayan sassauta kullen sa’o’i 24 da ya sa karamar hukumar Jos ta arewa sakamakon kashe mutane 37 a wuraren Yelwa Zangam dake Jos ta arewa.

Lalong ya ce farmakin karamar hukumar abu ne mai razanarwa da kuma tunatar da abubuwan takaici da suka faru a baya wadanda aka kusa mantawa dasu.

“Ku kula da yankunan ku saboda gwamnati ba za ta amince da karya doka ba a bisa ko wanne dalili saboda mulkinmu ya yi iyakar kokarin ganin ya kawo tsaro na tsawon shekaru 6 da suka gabata,” a cewarsa.

Sannan OPSH, rundunar dake kwantar da tarzoma a Filato da wasu bangarori na jahar Bauchi da Kaduna sun kori duk wani tsoro na batun wasu mutane masu kayan sojoni fa suka taru a Dutse Kura.

Jami’in labarai, Major Ishaku Takwa ya tattauna da manema labarai a yankin inda ya ce sun zagaye ko ina amma ba su ga ko makami guda daya ba.

A cewarsa,

“Rundunar ta isa Dutsen Kura kuma ta hada kai da shugabannin anguwanni inda suka bincike ko ina sannan suka tabbatar babu wani makami ko ‘yan ta’adda a yankin.

“Sannan OPSH sun kara rike wuta wurin ganin kawo karshen duk wasu ayyukan ta’addanci a jahar Filato.”

Takwa ya kara rokon mazauna yankin a kan su cigaba da samar da labarai da bai wa jami’an OPSH hadin kai don ba za su taba barin su kaskanta ba, kuma za su cigaba da kulawa da rayuka da dukiyoyin mazauna jahar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here