Lambobin Yabo ga Shugaban NITDA
Hoto Na Farko:- Ƙungiyar Injiniyoyin lantarki, Institute of Electrical and Electronic Engineers (IEEE), ne su ka karrama mai girma shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE), da lambar yabo, yau a wurin taronsu na shekara-shekara karo na huɗu domin yabawa haɗi da jinjina kan gudunmawar da ya ke ba su.
Mai girma ministan sadarwa da tattalin arziƙin fasahar zamani, Shaik, Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami, (FNCS, FBCS, FIIM), da ya miƙa masa lambar yabon, ya kasance babban baƙo mai gabatar da jawabi a wurin taron a bana, (2022).
Read Also:
Hoto Na Biyu: Ƙungiyar Jakadun jam’iyyar (APC), dangane da shugabanci nagari, “APC Ambassadors for Good Governance”, ita ce ta karrama mai girma shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE), da lambar yabo ta jinjina a gare shi akan ƙoƙarin da ya ke yi wajen cimma buri da manufofin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari (GCFR), kan tattalin arziƙin zamani.
Shugaban riƙo na sashen tsare-tsare na hukumar ta (NITDA), Dakta Aristotle Onumo, shi ne ya karɓi lambar yabon a madadinsa, jiya, a wurin babban taron ƙungiyar na ƙaddamarwa da rantsar da shugabanninta na Jihohi (36).