Lauyoyin Arewacin Najeriya 31 Sun Cin Alwashin Kare Abba Kyari a Gaban Kotu

 

Akalla lauyoyi talata da daya daga Arewacin Najeriya sun yanke shawaran kare DCP.

Abba Kyari a kotu Lauyoyin sun yi hakan ne matsayin amsa kiran gamayyar kungiyoyin arewa na karewa Abba Kyari hakkokinsa.

Barista Bappah Salisu, a madadin lauyoyin ya bayyana cewa kyauta zasu yi.

Abuja – Wani rahoton Vanguard ya nuna cewa akalla lauyoyin Arewacin Najeriya 31 sun alanta niyyar tsayawa mataimakin kwamishanan yan sanda Abba Kyari a kotu.

Lauyoyin sun yanke shawaran kare jami’in dan sandan ne bisa ga kiran gamayyar kungiyoyin Arewa inda ta bukaci a kare hakkokin Kyari.

Barista Bappah Salisu wanda ya bayyana hakan a jawabin da ya saki a Abuja ranar Laraba, 11 ga Agusta ya ce zasu kare Abba Kyari kyauta, ThisDay ta kara.

Salisu wanda yayi magana a madadin lauyoyin yace an zabesu daga jahohin Arewa daban-daban, kuma akwai kura-kurai a bukatar da FBI tayi na a turo mata Abba Kyari.

Abba Kyari ya sake gurfana gaban kwamitin bincike, an kwashe sa’a 4 yana shan tambayoyi

Abba Kyari, ya sha tambayoyi na sa’o’i hudu yayinda ya sake gurfana gaban kwamitin binciken kan alakarsa da shahrarren madamfari Ramon Abass aka Hushpuppi.

Ramon Abbas (Hushpuppi) wanda ake zargi da damfarar wani hamshakin attajiri, ya furta cewa ya ba Kyari cin hanci don kamo wani da ya nemi ya zarce shi a zambar dala miliyan 1.1.

Hukumar Bincike ta FBI, wata hukumar tabbatar da doka a Amurka ta zarge shi da hannu a wata harkallar damfara.

Ba tare bata lokaci ba IGP na yan sanda ya dakatar da Abba Kyari kuma aka saukeshi da jagoranci rundunar IRT.

Kwamitin binciken da Sifeto Janar na yan sanda ya kafa karkashin jagorancin DIG Joseph Egbunike, ta zauna ne a hedkwatan FCID dake unguwar Area 10 Garki Abuja.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here