Ahmed Lawan ya Karbi Hukuncin da Kotu ta Yanke na Soke Takararsa

 

Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Ahmed Lawan ya ce ya karbi hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya ce ba shi ne halattaccen dan takarar majalisar dattijai na jam’iyyar APC a mazabar Yobe ta Arewa ba.

Matakin na zuwa ne kwana guda bayan hukuncin kotun da ke zamanta a birnin Damaturu game da halattaccen dan takarar sanata a jam’iyyar APC daga mazabar Yobe ta Arewa.

Cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa nasada zumunta, Sanata Ahmed Lawan ya ce bayan tuntubar abokan harkar siyasa da magoya baya da abokan arziki, “Na yanke shawara ba zan daukaka kara a kan hukuncin ba. Na karbi kaddara”.

Sanarwar ta kunshi wani bayani mai alamta yin ban kwana, inda ya yi godiya ga shugabannin siyasar jiharsa ta Yobe da ma al’ummar mazabarsa da ya wakilta tsawon shekaru a majalisun tarayyar Najeriya.

Hukuncin Babbar Kotun Tarayya ya tabbatar da Bashir Sheriff Machina a matsayin halattaccen dan takarar sanata na jam’iyyar APC a mazabar Yobe ta Arewa.

Tun farko, jam’iyyar APC mai mulki ce ta miƙa sunan shugaban majalisar dattijai Sanata Ahmad Lawan ga hukumar zaɓe a matsayin ɗan takarar sanata mai wakiltar mazaɓar Yobe ta Arewa maimakon Bashir Machina, wanda ya ci zaɓen fitar da gwani na mazaɓar.

Shugaban majalisar na kasa Abdullahi Adamu ya yi iƙirarin cewa Sanata Ahmad Lawan ya sayi fom kuma ya shiga zaɓen fitar da gwani na sanatan Yobe ta Arewa, sai dai Bashir Machina ya ce shi kaɗai ya tsaya takara a zaɓen. Sai dai a ranar 21 ga watan Yunin 2022,

Bashir Sheriff Machina ya garzaya gaban kotu, yana kalubalantar matakin APC na aika sunan Sanata Ahmad Lawan, a matsayin dan takarar sanatanta na mazabar Yobe ta Arewa.

Ya dai ce shi ba zai janyewa kowa takararsa ta majalisar dattijai ba. Sanata Ahmad Lawan wanda ya shafe fiye da shekara 20 yana wakiltar al’ummarsa a Majalisar Wakilai da ta Dattijai, ya nemi takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, amma ya yi rashin nasara a hannun Bola Ahmed Tinubu. Kuma tun daga lokacin ne aka fara tababa game da makomar siyasar shugaban majalisar dattijan mai ci.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here