Babban Layin Wutar Lantarki na ƙasar ya Dauke Sau 98 Daga 2015 Zuwa 2022
Wasu bayanai da Jaridar Punch ta samu daga kamfanonin rarraba wutar lantarki a Najeriya, sun nuna cewa ƙarfin wutar lantarki na kasar ya ragu da megawatt 981.8 tsakanin shekarar 2015 zuwa watan Agustan 2022, duk da cewa gwamnatin tarayya ta zuba kudi da ya kai sama da tiriliyan biyu a bangaren, tun hawan Shugaba Buhari a 2015.
Sannan bayanan sunce babban layin wutar lantarki na ƙasar ya dauke sau 98 ƙarƙashin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.
Read Also:
Bayanan kamfanonin ya nuna cewa ƙarfin wutar lantarki na kasar yana megawatt 6,616.28 a 2015, inda ya sauka zuwa megawatt 5,634.47 a watan Agustan wannan shekara.
An kuma ruwaito cewa rashi da aka yi a bangaren na wuta tsakanin 2015 zuwa Agustan 2022 ya kai tiriliyan 1.76, inda masu gudanar da harkar ke ta nuna takaicin tabarbarewar al’amura a bangaren tun bayan raba masana’antar a watan Nuwamban 2013.
Har ila yau, bayanan sun nuna cewa wutar da ake samu a kasar ba ta wani inganta ba tun daga shekarar da ta wuce har zuwa wannan lokaci.