Legas: Kwamitin na  Binciken Cin Zarafin da ‘Yan Sanda su Kai

 

  Kwamitin da gwamnatin Jihar Legas ta kafa na jin bahasin abin da ya faru a harbe-harben da ake zargin sojoji sun yi yayin zanga-zangar EndSars a Legas ya ci gaba da zamansa a rana ta uku.

A jiya Juma’a ne kwamitin ya ziyarci Lekki Toll Gate a cigaba da binciken zargin harbin masu zanga-zangar, inda mambobin kwamitin suka ɗebo kwanson harsasai da aka harba kuma suka ce za a bincike su.

Tuni rundunar sojojin ta musanta zargin, tana mai cewa dakarunta ba su je wurin ba kwata-kwata sannan kuma ta ce Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ne ya nemi su fito tituna a ranar 20 ga watan Oktoba.

A zamansa na yau Asabar, kwamitin ƙarƙashin jagorancin tsohuwar Mai Shari’a Doris Okuwobi zai saurari ƙorafi huɗu.

Irin wannan kwamiti da wasu jihohi suka kafa ma sun fara nasu zaman, inda na Jihar Ogun ya ce ya karɓi ƙorafi 20 cikin mako biyu.

An kafa kwamitocin ne domin bincike tare da biyan diyya ga waɗanda ‘ya sanda suka ci wa zarafi ko kisa ba tare da haƙƙinsa ba a matsayin wani ɓangare na biyan buƙatun masu zanga-zangar neman gyara a ayyukan ‘yan sandan Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here