Cunkoso: Mutanen da Suka Rayu Shekara 20 a Legas Sun Cancanci Shiga Aljanna Kyauta – Gwamna El-Rufa’i

Gwamna Nasiru El-Rufa’i na jihar Kaduna ya ce wahalar da mutanen Legas ke sha wajen cunkoson ababen hawa na ba shi mamaki.

Gwamnan yace mutanen da suka rayu har tsawon shekar 20 a irin wannan yanayin lallai sun cancanci shiga Aljanna kyauta.

Malam ya bayyana manufofin gwamnatinsa na kawo tsarin aiki kwana hudu a mako, ya ce duk dan walwalar ma’aikata ne.

Abuja – Gwamnan Kaduna, Nasiru El-Rufa’i, ya ce mutumin da ya rayu tsawon shekara 20 a Legas, “Ya ci shiga aljanna kyauta” saboda wahalar cunkoson ababen hawa da ya sha fama da ita.

The Cable ta rahoto cewa Malam El-Rufa’i ya yi wannan furucin ne ranar Alhamis, a wurin taron manema labarai da tawagar yan Midiya na fadar shugaban ƙasa ke shiryawa a Abuja.

Da yake amsa tambayar meyasa gwamnatinsa ta rungumi aiki kwana huɗu a mako, gwamnan ya ce tsarin zai baiwa ma’aikata damar samun isasshen hutu tare da iyalansu.

Ya ce ma’aikata na fita aiki da karfin su ranar Litinin matukar suka samu gamsasshen hutu, inda ya kara da cewa al’ummar Kaduna na farin ciki da sabon tsarin.

Gwamnan ya ce:

“Amafanin tsarin shine mutane su samu hutu sosai, su samu karin lokaci tare da iyalansu, su samu karin lokacin shakatawa kuma su ci kuɗaɗen su.Hakan zai habaka tattalin arzikin mu.”

“Masu sha’awar haɗa wa da wasu sana’o’i kamar noma, za su samu lokaci. Kalubaen da muka fuskanta kan lamarin shi ne a bangaren ilimi, kuma tuni mun shawo kansa.”

“Mun gano cewa ana ɗaukar darasi na tsawon awanni 4 ne kacal ranar Jumu’a, dan haka muka ƙara awa ɗaya daga Litinin zuwa Alhamis, ba bashi kenan.”

Ina mamakin mazauna Legas – El-Rufa’i

Malam Nasiru ya ce yana matukar mamakin yadda mutanen Legas ke iya jure wa cunkoson ababen hawa, domin a cewarsa bai sani ba ko Asabar da Lahadi na gamsar da su wajen hutu.

“Ban san ya mutanen jihar Legas ke fama ba, kullum su kwashe awa 4 a wurin cunkoson ababen hawa har tsawon kwana biyar. Ban sani ba ko Asabar da Lahadi na isar su.

“Don haka nake ganin mutanen da suka rayu shekara 20 a Legas, kama ta ya yi su tafi kai tsaye zuwa Aljanna saboda sun daɗe suna rayuwa a wahala. Gaskiya sun biya, kamata ya yi su wuce kyauta.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here