Legas: Gwamnatin ta Gurfanar da ‘Yan Sanda 23 a Gaban Kotu #ENDSARS
Gwamnatin Jihar Legas ta fitar da sunayen ‘yan sandan da ta gurfanar a gaban kotu sakamakon cin zarafin mutane da kuma kisa ba tare da shari’a ba.
Baki ɗayan ‘yan sanda 23 da gwamnati ta wallafa sunayensu, ana tuhumarsu ne da laifukan da suka haɗa da kisan kai da kuma fashi da makami.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu ne ya wallafa sunayen da kansa yana mai cewa: “Barkanku da asuba jama’ar Legas, yau rana ce mai kyau ta fara sake gina Legas da kuma kawo ƙarshen cin zalin ‘yan sanda.
Read Also:
“Domin nuna jajircewarmu, ga jerin sunayen ‘yan sandan da muka gurfanar a gaban kotu sakamakon laifukan da suka shafi cin zarafin ɗan Adam.”
Wannan na zuwa ne yayin da jihohi ke ci gaba da kafa kwamitocin shari’a da za su binciki cin zarafin da ‘yan sanda suka aikata a kowacce jiha tare da biyan diyya ga waɗanda abin ya shafa, kamar yadda Majalisar Tattalin Arziƙi ta Ƙasa ta yi umarni.
Kafa kwamitocin wani ɓangare ne na matakan da aka ɗauka domin biya wa masu zanga-zangar EndSars buƙatunsu.
Da yammacin jiya Alhamis Shugaba Buhari ya buƙaci masu zanga-zangar su dakatar da ita sannan kuma kar su ɗauki rusa rundunar SARS da gwamnatin ta yi “a matsayin gazawa”.