Gwamnatin Legas ta Niƙe Baburan ‘Yan Achaɓa Sama da 2,000
Mahukunta a Legas sun soma aiwatar da dokar lalata babura ta hanyar niƙesu, inda ta soma da sama da dubu biyu da ta kwace a wannan mako.
Wani wani ɓangare ne na soma aiwatar da dokar haramta a-caɓa a birnin Jihar.
Read Also:
A watan da ya gabata aka bijiro da dokar kuma ta soma aiki a wannan satin a wani yunƙuri na ƙarawa jihar tsaro.
Wannan ba shi ne karon farko da gwamnati ta kakaba wannan haramci ba.
A Janairun 2020, gwamnati ta haramta hawa babura a wasu ƙananan hukumomi 15 na Jihar.
Wasu dai na nuna shaku kan ko dokar za ta ɗore, ganin alfanunsu da yanayin cunkoson a birni.