FIRS: Kotu ta Hana Jahar Legas da Rives Karbar Kudin Harajin VAT

 

Kotu ta umurci FIRS, Gwamnatin Legas da Gwamnatin Rivers kada su saka magana kan lamarin VAT.

Gwamnatin Rivers ta shirya tsaf don fara karban harajin VAT daga kamfanonin dake jahar.

Ba tare da bata Lokacin ba jahar Legas ta kafa sabuwar doka don yin haka itama.

Kotun daukaka kara dake Abuja ta dakatad da gwamnatocin jahar Rivers da Legas daga karbar kudin harajin VAT da hukumar FIRS ta saba karba daga hannun kamfanoni.

A hukuncin da Alkali Haruna Simon Tsanami ya yanke ranar Juma’a, ya bada umurnin cewa ayi watsi da sabuwar dokar da majalisar wakilan jahar Rivers ta kafa kuma gwamnan Wike ya rattafa hannu, rahoton DailyTrust.

Hakazalika majalisar dokokin Legas ta samar da irin wannan doka.

Amma hukuncin kotun daukaka kara ta fito yayinda gwamnan Legas, Babajide Sanwoolu, ke shirin rattafa hannu kan na Legas.

Hukumar samar da kudin shiga na Najeriya FIRS ta shigar da kara kotun daukaka kara kan hukuncin da wata kotu a Fatakwal ta yanke na halastawa jahohi karban harajin VAT.

Kotun na Legas a baya ta haramtawa hukumar FIRS da Antoni Janar na tarayya daga karban kudin harajin VAT daga wajen mazauna jahar Legas.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here