Gwamnatin Legas Zata Soke Biyan Tsofafin Shuwagabanni Fansho
Gwamna Babaajide Sanwo-Olu na jihar Legas yana son a dena biyan tsaffin gwanoni da mataimakansu kudin fansho.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin gababatarwa Majalisar Jihar kasafin kudin shekarar 2021 Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu a ranar Talata ya sanar da niyyansa na soke dokar biyan fansho na 2007 da ke bada damar biyan tsaffin gwamnoni da mataimakansu kudin fansho.
Read Also:
Ya sanar da hakan ne yayin da ya ke gabatar da kasafin kudi na shekarar 2021 da Majalisar Jihar Legas kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Sanwo Olu ya ce zai aike wa majalisar jihar Legas kudirin doka na neman amincewarsu game da batun.
A cewar Sanwo Olu, soke biyan tsaffin gwamnoni da mataimakan gwamnoni kudin fansho din zai rage kudaden da gwamnati ke kashewa.
Ya ce, “Mai girma Kakakin Majalisa da mambobin majalisa, bisa tsarin rage kudaden da gwamnati ke kashewa da yi wa talakawa aiki, za mu aiko da kudin dokar ga majalisa ne neman soke dokar (Payment of Pension Law 2007) da ta bada daman biyan tsaffin gwamnoni da mataimakansu kudin fansho.”