Legas: Har Yanzu Wuta na Cigaba da ci a Kamfanin Mai OVH
Gobara ta kama ma’ajiyar tankokin mai na OVH a unguwar Apapa, jihar Lagas.
Ba a san abun da ya haddasa gobarar ba wacce ke ci gaba da ci har yanzu.
Masu kashe wuta sun gaza kashe wutan bayan kwana daya da fara ci Sa’o’i 28 bayan daya daga cikin tankokin man kamfanin OVH ta kama da wuta a jihar Legas, har yanzu tana ci bal-bal. Wuta da ya fara ci misalin karfe 12 na ranan Alhamis, na ci har yanzu misalin karfe 4 na yammacin Juma’a.
Hakan na faruwa duk da cewa jami’an kashe wuta sun yi iyakan kokarinsu wajen kashe wutan.
Read Also:
A cewar hukumar kai agajin gaggawa ta jihar Legas LASEMA, ana kan kokarin kashe wutan yayinda ake yunkurin hana sauran tankokin kamawa da wuta.
Mun kawo muku rahoton cewa ma’ajiyar tankokin mai na OVH da ke yankin Apapa a jihar Lagas sun kama da wuta.
Ba a san ainahin abunda ya haddasa gobarar ba wacce ta fara ci a ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwamba ba.
Sai dai kuma masu aikin ceto na ta kokarin kwashe mutanen da ke cikin harabar wajen a lokacin da gobarar ta fara.
Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) na reshen, Ibrahim Farinloye, wanda ya tabbatar da afkuwar al’amarin ya ce an yi nasarar kwashe dukkanin ma’aikatan wajen.