Ahmed Lemu da Mahaifin Kwankwaso: Gbajabiamila ya Mika Sakon Ta’aziyyarsa
Femi Gbajabiamila ya yi alhinin mutuwar Sheikh Ahmed Lemu da Musa Sale Kwankwaso.
Kakakin majalisar ya yiwa mamatan samun jin kai daga Allah madaukakin sarki tare da samun Aljanna.
Gbajabiamila ya bayyana cewa ba za a taba mantawa da gudunmawar da mamatan suka bayar wajen ci gaban kasar ba Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya mika ta’aziyya ga iyalan marigayi Sheikh Ahmed Lemu.
Ya kuma yi ta’aziyya ga tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kan mutuwar mahaifinsa, Alhaji Musa Sale Kwankwaso.
Read Also:
A wata sanarwa dauke da sa hannun mai bashi shawara na musamman a kafofin watsa labarai a ranar Juma’a, Gbajabiamila ya bayyana marigayi shehin malamin wanda yayi rayuwa mai nagarta.
Ya bayyana cewa Sheikh Lemu, babban alkalin jihar Neja, ya yiwa al’umma hidima, inda ya kara da cewa ya kasance mutum mai aiki don hadin kai da zaman lafiya.
Gbajabiamila ya kuma bayyana cewa za a dunga tuna marigayin saboda gudunmawarsa ga addinin Islama da fannin ilimi, ba wai a jihar Niger kadai harma ga kasar baki daya.
Kan rasuwar mahaifin Kwankwaso, kakakin majalisar ya bayyana cewa Makaman Karaye ya yi rayuwa mai cike da nasara, indaa ya kara da cewa rashinsa abune mai matukar ciwo.
Ya yi addu’an Allah ya ji kan Sheikh Lemu da Alhaji Musa Saleh Kwankwaso a Jannatul Firdaus, jaridar Daily Trust ta ruwaito.