Korona: Jawabin Bill Gate Kan Afrika
Babban mai arzikin nan na duniya, Bill Gates, ya ce har yanzu duniya ta rasa dalilin da yasa korona bata yi kamari a Afrika ba.
Mashahurin mai kudin ya ce hakan yasa shi farin ciki domin hasashen da suka yi bai zamo gaskiya ba game da kasashen masu tasowa.
Ya ce ko a kasar Afrika ta Kudi da cutar ta fi kamari, babu rabin yawan masu cutar da mace-mace kamar Amurka.
Bill Gates, daya daga cikin shugabannin gidauniyar Bill da Melinda Gates (BMGF), ya ce har yanzu duniya ta kasa fahimtar dalilin da yasa masu korona a Afrika suka kasa yawa, The Cable ta wallafa.
Read Also:
Mai taimakon jama’an kuma dan Amurkan wanda yake saka hannayen jari a fannin lafiya ya ce, ya yi farin ciki da rashin hauhawar masu cutar a Afrika kamar yadda aka yi hasashe.
“Abu daya da nake farin ciki da rashin faruwar shine rashin tsanantar hauhawar cutar korona a kasashe masu tasowa,” ya rubuta a jawabinsa na karshen shekara.
“A halin yanzu, bai zama gaskiya ba hasashen. A kasashen Afrika, yawan masu kamuwa da cutar da mutuwar da ake saboda cutar bai kai Amurka ko Turai ba.
“Kasar da ta fi jin jiki a nahiyar ita ce kasar AFrika ta Kudu, amma ko a can din kasar bata kai Amurka ba da kashi 40 kuma yawan wadanda suka mutu basu kai kashi 50 na Amurka ba.”