Likita a Zambia ya Kuduri Aniyar Yin Tattaki Domin Haramta Shan Barasa

 

Wani likita a Zambia ya kuduri aniyar yin tattaki na nisan kilomita 140 (mil 87) da kafa domin janyo hankalin hukuma ta haramta shan giya a kasar.

Dakta Brian Sampa ya ce barasa ita ce sanadin da yawa daga cikin matsalolin da ake fama da su a kasar ta Zambia, wadda ke yankin kudancin Afirka.

Likitan wanda shi ne shugaban kungiyar likitoci masu neman kwarewa ya gaya wa BBC cewa, “Yawancin cin zarafin da ake yi wa mata a sanadiyyar buguwa da barasa ne, dukkanin cutuka da ake samu wadanda ba masu yaduwa ba ne suna da nasaba da giya, hatta larurar kwakwalwa tana da alaka yawanci da shan barasa.”

Brian ya ce, “Idan har muna son inganta abubuwa, dole ne a hana shan barasa, saboda kasuwanci ne da yake azurta wasu mutane ‘yan kalilan.”

Likitan ya fara tattakin nasa ne ranar Laraba daga babban birnin kasar Lusaka, inda ya nufi garin Kabwe da ke tsakiyar kasar. Ya shirya komawa babban birnin ta mota

Dakta Sampa wanda ya ce shirin nasa yana samun nasara, ya ce bayan kwana daya da fara tattakin ya wayi gari ranar Alhamis kafarsa ta kunbura amma duk da haka ya ce sai ya je garin da ya tsara zuwa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here