Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya ta yi Kira ga Likitoci Akan Suyi Hakuri su Koma Teburin sulhu
Yau Kwana na biyu da Likitoci a Najeriya suka sake shiga yajin aiki.
Likitocin sun zargi gwamnatin tarayya da rashin cika alkawuranta.
Gwamnatin tarayya na kira da Likitocin suyi hakuri su koma teburin sulhu
Abuja – Karamin Ministan Lafiya, Dr. Olorunimbe Mamora, a ranar Talata, ya yi kira ga shugabannin kungiyar Likitoci masu neman kwarewa NARD su koma teburin sulhu.
Read Also:
Gwamnati tace tana iyakan kokarinta wajen canza tunanin da ake mata a bangaren lafiya. Mamora ya bayyana hakan ne a taron kungiyar likitoci NMA, shiryar birnin tarayya, rahoton Punch.
Tace:
“Gwamnati na kokarin kawo gyara. Ba zai yiwu muyi kasa a gwiwa ba. Ina amfani da wannan dama in yi kira ga Likitocin dake yajin aiki yanzu su dawo teburin sulhu saboda a tattauna dukkan matsalolin.”
“Wannan shine roko na. Ko a faggen yaki, abokan adawa a karshe na komawa teburin sulhu domin tattauna matsaloli.”