NARD: Likitoci Sun Janye Yajin Aiki

Likitoci masu neman kwarewa a Najeriya sun janye yajin aikinsu a wannan Larabar.

Tun a ranar 2 ga watan Agusta suka tsunduma yajin aikin, sai dai a cewar shugaban kungiyar likitocin Dr Godiya Ishaya, sun yanke wannan hukuncin ne bayan jimma wasu daidaito.

Likitocin sun ce yajin aikin nasu ya yi tsayi ne saboda kin amincewar gwamnati da wasu bukatunsu.

Yanzu dai an tsayar cewa nan da mako shida za a sake hawa teburin tattaunawa domin sake nazari da ganin cigaba da aka samu tsakaninsu da gwamnati.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here