Gina Kasa: Jam’iyyar APC Reshen Ingila ta ba wa Shugaba Buhari Lambar Yabo

 

Jam’iyyar APC a kasar Ingila ta karrama shugaba Buhari da lambar yabon shugaba mai gina kasa.

Hakazalika, Bola Tinubu shi ma an bashi lambar yabon kasancewa shugaba mai tasiri a duk dai a APC ta Ingila.

Wannan na zuwa ne a cikin bukukuwan cikar Najeriya shekaru 61 da ‘yanci a wannan shekarar ta 2021.

UK, Landan – An bai wa Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) lambar yabo ta shugaban da ya gina kasa a wani taron da Jam’iyyar APC, reshen Ingila ta shirya, don murnar cikar Najeriya shekaru 61 da samun ‘yancin kai a London.

Sakataren Yada Labarai na kungiyar, Jacob Ogunseye, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka aikewa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Lahadi 3 ga watan Oktoba a Abuja, Vanguard ta rawaito.

Ya ce an kuma zabi Jagoran Jam’iyyar na Kasa, Bola Tinubu don bashi lambar yabo ta Shugabanci a taron da aka yi ranar 2 ga Oktoba, a Dorchester Hotel da ke Landan a kasar Ingila.

A cewar sanarwar, duk da kalubalen da kasar ke fuskanta a yanzu, makomarta tana da haske mai gamsarwa, ta kara da cewa ya kamata a dauki ranar ‘yancin kai a matsayin ranar tunawa kan abubuwan da suka gabata na kasar, yin aiki akan halin da ake ciki da tsara makoma.

Punch ta tattaro sanarwar ta nakalto shi yana cewa:

“Lokaci ya yi da za a sake yin aiki, sake-jaddadawa, dubawa da sake fasalin kasar don bunkasa tattalin arzikin kasa da kuma tsarin aiki don tabbatar da kyakkyawan yanayin rayuwa ga daukacin ‘yan kasa.”

Jagoran na APC ingila ya lura cewa mai yiwuwa Najeriya ba ta kasance a inda ya kamata ba a matsayin kasa, amma dai a yanzu ta fi da.

“Mun tsallake halin nadama da hadari da muke ciki kuma yanzu muna samun ci gaba mai yawa tare da sabon tsari a rundunar sojoji da ta sake samun karfafawa.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here