Kungiyar Likitoci NARD ta Mayarwa da Kotu Martani Kan Umarnin Komawa Bakin Aiki

 

Kungiyar Likitoci NARD tace sam bata san da cigaba da zaman kotu ranar Litinin ba.

Shugaban kungiyar, Uyilawa Okhuaihesuyi, yace kungiyar ta ga rahoton zaman a shafukan jaridu.

Shugaban ya kara da cewa yajin aikin su na nan ba gudu babu ja da baya har sai gwamnati ta biya musu bukatunsu.

Abuja – Kungiyar likitoci masu neman kwarewa (NARD) ta maida martani kan hukuncin kotun ma’aikata “mai rikitarwa” na ranar Litinin.

Legit.ng Hausa ta ruwaito muku cewa kotun dake zamanta a Abuja ta umarci ɓangarori biyu, gwamnati da NARD, su jingine duk wani rashin jituwa su rungumi sulhu.

Da yake zantawa ta wayar salula da wakilin Premium times, shugaban kungiyar NARD, Uyilawa Okhuaihesuyi, yace kungiyarsu ta ga labarin zaman kotun ne a shafukan jaridu.

Bamu san da zaman kotu ba

Okhuaihesuyi yace:

“Bamu san an yi wani zama ba, mun ji labarin ne a kafafen watsa labarai kuma shiyasa ma bamu halarci zaman kotun ba.”

Yace abinda kungiyarsu take da masaniya shine an ɗage sauraron shari’ar har zuwa 15 ga watan Satumba.

Yajin aiki ba gudu ba ja da baya Mista Okhuaihesuyi ya musanta jita-jitar cewa kotu ta umarci likitocin su janye yajin aiki kuma su koma bakin aiki.

Yace yajin aiki ba gudu ba ja da baya har sai lokacin da gwamnatin tarayya ta biya musu bukatunsu.

Wane umarni kotu ta bayar?

Sabanin rahoton da wasu kafafen watsa labarai suka buga, Premium times ta rawaito cewa mai shari’a, John Targema, ya yi fatali da bukatar dakatar da likitocin daga yajin aikin da suke.

Wannan shine karo na biyu da alkalin ya yi fatali da makamanciyar wannan bukatar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here