Kano: Likitocin Manyan Asibitoci za su Fara Yajin Aiki

 

Kungiyar likitoci da ke aiki a manyan asibitocin gwamnatin jihar Kano sun yi barazanar tsundunma yajin aiki na tsawon mako biyu daga gobe Talata.

Kungiyar ta ce gazawar da gwamnatin Kano da ke arewacin Najeriya ta yi wajen aiwatar da wasu daga cikin yarjejeniyar da suka cim ma tun a Satumban 2023, da ƙarancin likitoci a jihar na daga cikin dalilan shiga yajin aiki.

Kazalika, ƴan ƙungiyar sun ce akwai batutuwan da suka shafi rashin kayan aiki, da ƙarancin ma’aikata, da kuma ƙarancin albashi.

Shugaban ƙungiyar Dr. Anas Idris Shanono ya faɗa wa BBC cewa 4 ga watan Agusta suka kafa kwamatin tattaunawa da gwamnatin.

“Idan ka kalli likitocin da ke Kano 600 ne da ‘yan kai, hakan na nufin kowane likita na kula da sama da mutum 30,000 kenan,” in ji shi. Ya ƙara da cewa sun lura albashin da ake biyan likitocin a wasu jihohi ya zarta na Kano.

Sai dai ƙungiyar ta ce duk da cewa da gwamnatin baya suka cim ma yarjejeniyar ya kamata gwamnatin yanzu ƙarƙashin jam’iyyar NNPP mai adawa a Najeriya ta saurare su.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here