ALLAH ya yi wa Babban Limamin Masallacin Juma’a Dake Kaduna, Sheikh Dahiru Lawal Abubakar Rasuwa

 

Malam Dahiru Lawal Abubakar, babban limamin Masallacin Juma’a na titin Maiduguri dake garin Kaduna ya riga mu gidan gaskiya.

Alkalin wata babbar kotun shari’a dake karamar hukumar Makarfi ta jihar Kaduna, ya rasu sakamakon gajeriyar rashin lafiya.

Malamin ‘da ne ga fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Lawal Abubakar, kuma ya rasu yana da shekaru 52 a duniya.

Kaduna – Babban limamin masallacin Juma’a na titin Maiduguri a cikin garin Kaduna, Malam Dahiru Lawal Abubakar, ya rasu yana da shekaru 52 a duniya.

Daily Trust ta tattaro cewa, babban limamin wanda kafin rasuwarsa, alkali ne a babbar kotun shari’a dake kaamar hukumar Makarfi ta jihar Kaduna, ya rasu sakamakon gajeriya rashin lafiya.

Ya yi jinyar a asibtin 44 na sojoji kafin ya rasu a sa’o’in farko na ranar Laraba.

Babban limamin ‘da ne ga fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Lawal Abubakar, kuma yayan daya daga cikin tsoffin editocin Daily Trust mai suna Malam Nasiru Lawal Abubakar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here