Lokuta da Wurare da Masu Zanga-Zanga za su Fito a Watan Oktoba
FCT, Abuja – Masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa sun kara shirin fitowa kan titunan Najeriya domin nuna fushinsu kan gwamnati.
An samu sabani tsakanin jam’iyyun siyasa a Najeriya a kan fitowa zanga zangar a ranar yancin kasa.
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore ya wallafa wasu wuraren da za su taru domin fara zanga zangar a shafinsa na Facebook.
Wasu wurare da lokutan zanga zanga
Punch ta ruwaito cewa masu zanga zangar sun ce za su taru a dandalin Eagle Square a birnin tarayya Abuja.A Legas kuma za su taru a karkashin gada a Ikeja.
Read Also:
A jihar Oyo, matasan sun ce za su fito zanga zangar ne da misalin karfe 8:00 na safe a shatale-talen Mokola da ke Ibadan.
Omoyele Sowore ya bayyana cewa suna shirye tsaf domin fara zanga zangar da misalin karfe 7:00 na safe a Abuja sai kuma Legas za su fito karfe 7:30 na safe.
APC ta yi gargadi kan zanga zanga
Daraktan yada labaran APC, Bala Ibrahim ya ce kada matasa su rudu da yan adawa wajen fitowa zanga zanga a Najeriya.
Sai dai daraktan yada labaran PDP, Abdullahi Ibrahim ya ce APC ke azabtar da mutane a Najeriya saboda haka ne matasa suka fito zanga zangar.
Haka zalika daraktan yada labaran LP, Obiora Ifoh ya ce ba wanda zai zargi jam’iyyun adawa da shirya zanga zangar saboda APC ce ta jefa mutane a damuwa.