Kungiyar Kwallon Lyon ta Fadi Dalilin Sallamar Marcelo

Marcelo, dan kasar Brazil ya rasa matsayinsa a kungiyar kwallon Lyon sakamakon laifin tusa bainar jama’a.

Rahotanni daga faransa sun nuna cewa ya fusata hukumomin kungiyar kwallon ne bayan tusa a dakin shiryawa.

An tattaro cewa wannan ya biyo bayan kashin da Lyon ta sha 3-0 hannun kungiyar Angers.

Kungiyar kwallon Olympique Lynonnais dake kasar taka leda a Ligue 1 a Faransa ta sallami dan wasanta, Marecelo, bayan barka tusa a dakin shiryawan yan kwallo kuma ya fara dariya.

Lyon a watan Agustan da ya gabata cewa an dakatad da dan kwallon kuma an rage masa matsayi bisa dabi’ar da bai dace ba.

A cewar L’Equipe, Marcelo dan shekaru 34 ya barka tusa ne bayan wasa da kungiyar Angers, inda Lyon ta sha kashi kuma Marcelo yaci gida “Own Goal” a wasar.

An ruwaito cewa bayan fushin da ake da shi bisa cin gidan da yayi, ya barka tusa a dakin ‘dressing room’ sannan kuma ya fara dariya.

Diraktan harkokin horo na kungiyar, Juninho ya dakatad da Marcelo. Daga baya kuma aka sallamesa a watan Junairu.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here