Jiga-Jigan Jam’iyyar PDP za su yi Taro Gabanin Taron Zaben Fidda Gwani

Gabanin taron zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP, jiga-jigan jam’iyyar za su zauna don dinke barakar jam’iyyar.

Ana sa ran za a yi taron da yammacin yau Laraba bayan dage lokacin yinsa daga karfe 10 na safiyar yau dinnan.

Rahoton da muka samo ya bayyana sabon jadawalin tarukan da za a yi a lokuta mabambanta a yau Laraba.

Abuja- Gwamnonin jam’iyyar PDP sun shirya yin wani taro a wani zama na hadin gwiwa a Abuja gabanin babban taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar na kasa a yau.

Taron an ce zai gudana ne a masaukin Gwamnan Jihar Benue da ke Asokoro, inji rahoton Tribune Online.

Tuni dai akasarin shuwagabannin jam’iyyar na jihohi da jiga-jigai suka isa wurin taron wanda aka ce zai gudana da yammacin yau dinnan.

Babban manufar taron dai ana tunanin shi ne batun raba tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa a zaben 2023 mai cike da takaddama.

Gwamnan da ya karbi bakuncin taron, Samuel Ortom, shi ne shugaban kwamitin shiyya na jam’iyyar PDP, wanda ya kasa cimma matsaya kan lamarin.

PDP ta dage taron da aka shirya yi a yau Laraba

Sai dai, wnai rahoton Vanguard ya ce, shugabancin jam’iyyar PDP ya sauya jadawalin taron na kwamitin amintattu na kasa da na majalisar zartarwa ta kasa ta PDP da aka shirya gudanarwa tun daga karfe 10 na safe zuwa 2:00 na rana.

Amma an yi ganawar bayan labule da fitattun ‘yan jam’iyyar da suka hada da tsaffin shugabannin majalisar dattawa, David Mark da Bukola Saraki, da shugaban BoT Sen. Walid Jibrin.

Hakazalika da gwamnonin Edo, Enugu, Adamawa, Taraba mai masaukin baki, Samuel Ortom, da sauran su, kimanin awanni biyu kafin gabatar da shirin taron da misalin karfe 12:00 na rana.

Duk da cewa ba a fitar da wata sanarwa a hukumance ba, Vanguard ta tattaro cewa taron wanda zai dauki tsawon sa’o’i kadan zai bada damar tattaunawa kan batutuwa masu sarkakiya.

A bisa sabon tsarin jadawalin taron, za a fara taron kwamitin da karfe 4:00 na rana, za a yi taron na BoT da karfe 7 na dare yayin da ake shirin gudanar da taron na NEC zai fara da karfe 8:00 na dare.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here