Ma’aikatan Majalisar Dokoki Sun Koka da Rashin Biyan Albashi
Wasu daga cikin ma’aikatan Majalisar Dokoki ta kasa sun koka dangane da rashin albashi.
Ma’aikatan sun bayyana kusan shekara uku kenan ba su karbi albashi a Majalisar ta Dokoki ba.
Daraktan, Hulda da Jama’a, a NASC, Misis Janet Mambula, a ranar Litinin ta ce, ana bincike kan lamarin albashin.
Wasu daga cikin ma’aikata 355 da aka dauka tun shekarar 2017 da Hukumar Kula da Ayyukan Majalisar ta yi ikirarin a ranar Litinin cewa har yanzu suna jiran albashi.
Binciken da wakilin jaridar The Punch ya gudanar ya nuna cewa yawancin ma’aikatan da abin ya shafa ba su samu albashi ba tun lokacin da aka dauke su sama da shekaru uku da suka gabata.
An gano cewa hukumar, wani lokaci a cikin 2017, ta fara aiki don maye gurbin wasu mambobin da suka yi ritaya ko barin aikin.
Wasu daga cikin wadanda suke cikin tsarin a matsayin masu taimaka wa majalisa ba tare da wasikar nadi ba.
Sauran wadanda suma suka gabatar da bukatar su ne wadanda suka yi hidimarsu ta matasa a Majalisar Dokoki ta Kasa, amma har yanzu suna jiran tsammani ne bayan an kammala shirin na shekara guda, suna neman ayyukan yi.
Yawancinsu an ce an ba su wasikar nadin, wanda daga baya aka janye su lokacin da ba a yi wani tanadi game da albashin ba.
Read Also:
Ma’aikatan da abin ya shafa sun ce sun kasance a cikin tsarin har tsawon shekara guda har zuwa watan Yulin 2018 lokacin da Hukumar Kula da Majalisar Dokoki ta kasa ta ba su sabbin wasikun nadin.
Wasu daga cikin ma’aikatan wadanda suka zanta da wakilin The Punch da sharadin a sakaya sunan su don kaucewa takunkumi, duk da haka, sun ce kadan ne daga cikin su aka biya bayan an tabbatar da nadin nasu.
Wani babban jami’in hukumar ta NASC, wanda tun farko ya zanta da wakilin The Punch a kan kada a bayyana sunansa, ya danganta jinkirin biyan albashin ma’aikatan da raguwar kudaden shiga.
Ya ce, “Mun dauki ma’aikata kusan 250. Wadanda suka fara a watan Disambar 2017 sun fara jin dadin albashi watanni uku bayan haka.
“Wadanda Majalisar ba ta dauke su aiki yadda ya kamata a shekarar 2017 an dauke su aiki a cikin watan Yulin 2018. Sun tsaya shekara guda kafin a ce su ci gaba a shekarar 2019.
“Na fahimci dalilin da ya sa ba a ambaci sunayensu a cikin kasafin kudin 2018 ba; wannan shine dalilin da ya sa ya dauki kimanin shekara guda kafin mu nemi su ci gaba.
“Yawancinsu sun ci gaba da zuwa ofishin ko da a ka janye wasikun nada su.
“Mun roke su da su jira har sai lokacin da za a ambaci sunayensu a cikin kasafin. Wasu daga cikinsu da suke bayar da muhimman ayyuka ana biyansu alawus daga alawus dinmu. ”
Amma Daraktan, Hulda da Jama’a, a NASC, Misis Janet Mambula, a ranar Litinin ta ce, “Hukumar tuni ta fara binciken lamarin.”
Lokacin da aka nemi da a yi karin haske a kan matakan da ake dauka da kuma yawan wadanda abin ya shafa, Mambula ta ce, “Lokacin da na ce hukumar na bincika wa, kawai ku dauka cewa muna aiki a kai.”