Mace ‘Daya ba za ta Iya da Kaifin Basira ta ba – Mai Mata 15 da Yara 107
David Sakayo Kaluhana, dattijo ne mai matan aure 15 da kuma yara guda 107.
Magidancin wanda ke alfahari da kansa ya bayyana cewa ya auri mata da yawa ne saboda mace daya ba za ta iya da kaifin basira irin nasa ba.
Duba ga yawan iyalinsa, mutum zai ta mamaki ta yadda David ke iya daukar dawainiyarsu kuma ya magantu a kan haka.
Wani dattijo mai shekaru 61 mai suna David Sakayo Kaluhana wanda ke da matan aure 15 da yara 107 ya yi fice kuma ya haddasa cece-kuce a yanar gizo.
A wata da aka yi da shi, David ya fada ma Afrimax cewa akwai yiwuwar zai sake auren wasu matan kuma ya bayyana maza masu mata daya a matsayin marasa wayo.
A cewarsa, tsananin wayo irin nasa ya fi karfin ya auri mace guda daya kuma wannan ne dalilin da yasa ya tara iyali mai yalwa.
“Wannan kai irin nawa mace daya ba za ta iya sarrafa shi ba saboda yana dauke da manyan abubuwa da ba za ta iya dauka ba.
“Wannan ne dalilin da yasa na auri mata da yawa saboda wayona ya fi karfin mace daya.”
Daya daga cikin matan David ta magantu Jessica Kaluhana, daya daga cikin matan David ta jinjinawa maigidan nata yayin da Afrimax ta zanta da ita.
Read Also:
Jessica ta ce ta auri David a 1998 kuma sun haifi yara 13 tare, inda 11 daga cikinsu ke raye har yanzu.
Sabanin abun da mutane da dama ke tunani, Jessica ta bayyana cewa iyalin na zaman lafiya. Ta ce:
“Muna zaune lafiya kuma cikin kaunar juna. Ina kaunar mijina sosai.
“Ban taba kishin ganinsa da wasu matan ba. Mutum ne mai mutunci. Duk abun da ya yi yak an zama daidai a koda yaushe domin yana tunani sosai kafin ya aikata abu.”
Kan yadda David ke ciyar da iyalinsa, Afrimax ta rahoto cewa shi masanin tarihi ne kuma yana samun kudi wajen fadama mutane tarihi.
Mutane sun yi martani a soshiyal midiya
Elizabeth Otieno Nyaure ta ce:
“Na fito daga gidan mata da yawa kuma iyalin na cikin aminci. Mata da yara na wahala kuma ana yi masu fin karfi.”
Immaculate Nyongesa ya ce:
“Da zaran yam utu za mu samu marayu fiye da 200 da zaurawa 50 shin wayonsa ya taba shawartansa a kan makomar wadannan yaran, Solomon na da arziki na tausayawa wadannan mata da idanunsu suka rufe.”
Ann Mccurdy ya ce:
“Kawai dai ina fatan iyaye matan na tura dukka yaran nan makaranta don su samu ilimi su iya banbance fari da baki sannan su ceci kansu daga wadannan tsoffin da suka kange su a cikin datti. Ya ku yan mata ku ilimantar da kanku sannan ku yantar da kanku.”