Macizai Sun Addabi Jami’ar Umaru Yar’ adua Dake Jahar Katsina
Macizai sun addabi jami’ar Umaru Yar’ adua dake jahar Katsina, lamarin da yake haifan dardar.
A halin yanzu, jami’ar ta dauki matakin ci gaba da feshin maganin dabbobi domin fatattakar macizai.
Jami’an ta bayyana cewa, tana kuma sare bishiyoyi da shukoki domin tabbatar da aminci a jami’ar.
Katsina- Hukumar jami’ar Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina, a ranar Talata 7 ga watan Satumba, ta ce ta yi feshin magani a babbar harabar jami’ar don kubuta daga macizai da sauran nau’ikan dabbobi wadanda ka iya cutar da dalibai da sauran membobin jami’ar.
A karshen makon da ya gabata, wani faifan bidiyo da ke nuna wani kumurcin maciji da aka kama a cikin Sabbatical Quarters na jami’ar ya yadu a kafafen sada zumunta, Punch ta rawaito.
A cikin wata sanarwa a ranar Talata mai dauke da sa hannun Shugaban Hulda da Jama’a na jami’ar, Mallam Abdulhamid Danjuma, ta ce an yi feshin magani a harabar jami’ar.
Sanarwar ta karanta a wani bangare:
Read Also:
“A kokarin kawar da macizai da sauran dabbobi masu rarrafe a cikin harabar gaba daya, gudanarwar jami’ar Umaru Musa Yar’adua ta Jihar Katsina, ta yi nasarar korar dimbin macizai a cikin harabar cibiyar.
“Kokarin ya yiwu ne ta hanyar daya daga cikin atisayen da ake yi na yau da kullum da ake gudanarwa a cibiyar.
“A ka’ida, hukumomin jami’ar galibi suna gudanar da atisayen feshin magani bayan mako biyu don fatattakar dabbobi masu rarrafe, macizai da sauran kwari don sanya jami’ar zama wuri mai aminci ga ma’aikata, dalibai da baki.
“Baya ga feshin maganin, ana sassare bishiyoyi da shukoki don kawata kewayen jami’ar da korar dabbobi masu rarrafe da sauran beraye saboda membobin jami’ar su sami kwanciyar hankali da tafiya cikin walwala ba tare da wani fargaba ba.
Hakazalika, sanarwar ta bukaci dalibai da sauran mazauna jami’ar da su kasance masu kai rahoto ga hukumar makaranta duk lokacin da suka ga wani abu da basu fahimta ba na dabbobi kasancewar ana tsakiyar damina.
A bangare guda, jami’ar ta ba da tabbacin kare rayuka da lafiyar mazauna jami’ar, inda sanarwar ta ce:
“Jami’ar tana ba da tabbacin cewa za ta ci gaba da kare rayukan ma’aikatanta, dalibai da sauran baki ta hanyar yin aiki tukuru don magance duk kalubalen da ke iya zama barazana ga rayuwar cikin harabar.”