Madatsun Ruwan Kano na Buƙatar Gyara – Gwamnatin Jihar
Kwamitin da gwamnatin Kano ta kafa don duba halin da madatsun ruwan jihar ke ciki ya tabbatar da cewa wasu daga cikin madatsun ba su fuskantar barazanar ɓallewa.
Gwamnati ta ce ta ɗauki matakin tura jami’ai su gudanar da bincike ne sakamakon ambaliyar ruwan da aka samu a jihar Borno sakamakon madatsar ruwan Alau da ta ɓalle
Jihar Kano na da ɗumbin madatsun ruwa da ake amfani da su wajen noman rani da kuma samar da ruwan sha ga al’ummar jihar.
Kwamashinan Ruwa Ali Haruna Makoɗa ne ya jagoranci tawagar zuwa manyan madatsun ruwan.
Read Also:
“Jiya [Litinin] mun je Tiga, yau kuma mun zo Watari. Mun ga wurin da idan ya cika ake fitar da ruwan kuma lafiya yake…Amma mun ga wurin da zaizayar ƙasa ta ɗan shafi wurin,” in ji shi.
Bayanai sun nuna cewa Kano na da manyan madatsun ruwa 19 mallakar gwamnatin jihar da ta tarayya, da kuma 46 ƙanana.
Injiniya Marwan Ahmad Aminu, shi ne kwamashin ma’aikatar ayyuka, kuma ya ce sun lura akwai ‘yar matsala a jingar da aka yi wa madatsar ruwa ta Tiga.
“Mun ga akwai ‘yar matsala amma dai ba wata gagarumar matsala ba ce, kuma muna da bayanin cewa gwamnatin tarayya ta turo tawagar da za ta yi wannan gyaran,” a cewarsa.