Muna Magana ne Akan Darajar Mutum a Idon Jama’a, da Irin Bata Masa Suna da AKai – Lauyan Tsohon Shugaban EFCC

 

Ibrahim Magu ya na kukan ba ayi masa adalci a binciken da aka yi a EFCC ba.

Wani Lauyan tsohon shugaban na EFCC, Tosin Ojaomo neya yi magana a yau.

Tosin Ojaomo ya ce ba ayi wa Magu da sauran Jami’an da aka bincika adalci ba.

Lauya mai kare tsohon mukaddashin shugaban EFCC, Tosin Ojaomo, ya ce ba ayi adalci a game da lamarin Ibrahim Magu da wasu abokan aikinsa ba.

Jaridar The Nation ta fitar da rahoto cewa, Tosin Ojaomo, ya yi wannan magana ne a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin a ranar Lararar nan.

Mista Ojaomo yake cewa: “Kwatsam sai ga rahoto ya fito, an yi wani sabon nadin mukami… gaskiya ba ayi wa Magu adalci a kan lamarin nan ba.”

“Mu na magana ne a kan darajar mutum a idon jama’a, da irin bata masa suna da aka yi a waje.”

Lauyan ya na magana ne a kan kwamitin binciken da shugaban kasa ya nada karkashin Ayo Salami domin a gano gaskiyar zargin da ke kan wuyan Magu.

Masanin shari’ar yake cewa bayan Ibrahim Magu, an dakatar da sauran wasu jami’an EFCC a sakamakon binciken da kwamitin Ayo Salami ya gudanar.

Bayan an kammala wannan aiki, Ojaomo ya ce yanzu kamar ba ta wadannan jami’ai ake yi ba.

“Ba maganar Magu ba ce kawai, akwai mutane a hukumar da aka dakatar, duka wadannan mutane kallon mutuncin da ake yi masu ya na fuskantar barazana.”

Ojaomo ya so ace an fito an yi bayanin abin da kwamitin binciken da aka kafa su ka gano, domin a wanke Magu, ko kuma a tabbatar da duk zargin da ke kansa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here