Abba Yusuf Bichi ya Magantu Kan Sabani Tsakanin Matar Shugaban Hukumar DSS da ‘Dan Takarar NNPP na Jihar Kano
An samu sabani tsakanin mai dakin Darekta Janar na DSS da ‘dan takaran NNPP a filin jirgin sama.
Abba Yusuf Bichi ya ce matar shugaban hukumar DSS ba ta umarci a cafke Abba Kabir Yusuf ba.
‘Dan wasan kwallon ya zargi Gida Gida da cin mutuncin Aisha Yusuf Bichi, har abin ya zama fada.
Abuja – Abba Yusuf Bichi wanda mahaifinsa yake rike da kujerar shugaban hukumar DSS na Najeriya, ya yi magana a kan wasu rahotanni da ke yawo.
A farkon makon nan aka rika yada labari cewa an samu takaddama tsakanin matar shugaban DSS da ‘Dan takarar Gwamna a Kano, Abba Kabiru Yusuf.
Abba Yusuf Bichi ya yi amfani da shafinsa na Twitter, ya bada na shi bangaren labarin rigimar, ya yi magana ne a daren yau
@Abba_YusufBichi.
Read Also:
A cewarsa, mai dakin shugaban hukumar DSS ba ta umarci jami’an tsaro na fararen kaya su cafke Abba Kabiru Yusuf wanda ake kira Abba Gida Gida ba.
Haka zalika, matashin ya ce Aisha Yusuf Bichi ba ta umarci a kashe hadimin ‘dan takaran ba.An ga hotunan Garba Kilo da alamar yi masa jina-jina.
Maganar Abba Yusuf Bichi a Twitter
“‘Yan daban Abba Gida Gida ne suka tare tawagar motocin Mai dakin Darekta Janar na DSS, sai jami’an DSS su ka nemi shiga filin jirgi, amma suka hana su.
Jami’an tsaron sun tunkare su, amma sai ‘yan daban suka tada rigima, yayin da duk ake yin wannan, Abba Gida Gida yana zaune cikin motarsa yana kallo! Da DSS suka sake yunkurin shiga filin tashin jirgin, sai Abba (Gida-Gida) ya fito, yana cin zarafin jami’an, sannan ya umarci ‘yan dabansa su tada rigima.
Bayan ganin abin da yake faruwa, sai mai dakin Darekta Janar ta sauko daga motarta, ta roki Abba Gida Gida, sai ya koma kan motar, ya shiga zaginta. Daga nan wani daga cikin ‘yan dabansa ya nemi ya aukawa matar DG, a nan ne jami’an DSS da ke tsaron ta suka maida martani, har ya samu rauni.”
– Abba Yusuf Bichi