Manjo Janar Bashir Magashi da Sauran Hafsoshin Tsaro Sun Kai Ziyara Maiduguri

 

Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya tare da sauran hafsoshin tsaro sun isa Maiduguri dake jahar Borno.

Ministan tsaro tare da sauran hafsoshin tsaron kasar sun isa ne domin yanayin barnar da Boko Haram suka tafka.

Dakarun sojin kasar ta bakin kwamandan OPD, ya jinjinawa hafsoshin tsaron da ministan a kan ziyarar da suka kai Ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya, a ranar Lahadi, ya dira Maiduguri tare da rakiyar shugaban ma’aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor tare da sauran hafsoshin tsaro, domin duba yanayin barnar da ‘yan Boko Haram suka yi a jahar.

A yayin karbar ministan da tawagarsa a hedkwatar Operation Lafiya Dole a Maiduguri, kwamandan rundunar Manjo Janar Farouq Yahaya, ya jinjinawa yadda minstan, shugaban ma’aikatan tsaro da sauran hafsoshin tsaro ke nunawa.

Ya ce dakarun suna godiya ga ministan a kan ziyarar suke kai musu tare da tabbatar da cewa ministan tare da sauran shugabannin tsaron sun ziyarcesu bayan nada su da aka yi.

Kamar yadda Vanguard ta wallafa, Yahaya yayi bayanin cewa bayan ziyarar da shugabannin tsaron suka kai karkashin shugabancin shugaban ma’aikatan tsaro, sauran shugabannin tsaro sun kai ziyara daya bayan daya.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa ministan da tawagarsa sun shiga taron sirri tare da kwamnadojin hedkwatoci.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here