Rundunar ‘Yan Sandan Jahar Neja ta Kashe ‘Yan Bindiga 6

 

Rundunar ‘yan sanda a jahar Neja ta hallaka ‘yan bindiga 6 a wani samame kan ‘yan bindiga.

An bayyana mutuwar hudu daga ciki nan take, biyu kuwa an tsince su a daji matattu murus.

Rundunar ‘yan sandan jahar har zuwa yanzu basu fidda wata sanarwa game da lamarin ba Rundunar tsaro ta hadin gwiwa a karamar hukumar Shiroro da ke jahar Neja ta kashe ‘yan bindiga shida a yayin wani samame na dakile harin da ‘yan ta’addan suka kai a yankin Garkogo, The Nation ta ruwaito.

An ce ‘yan bindigar sun kai hari a wasu kauyukan da ke kusa da Garkogo amma rundunar hadin gwiwar ta fatattake su.

Bayanai sun ce rundunar ta dauki matakin ne bayan wani labari da ta samu kan harin da aka kai kauyukan a safiyar ranar Asabar inda suka yi kwanto da ‘yan bindigan.

An ce wasu ‘yan bindigan da dama sun tsere da munanan raunuka na harsashi kamar yadda suka gudu daga kauyukan a kan babura.

Wannan nasarar ta rundunar tsaro ta hadin guiwa na zuwa ne makonni uku bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari sansanin rundunar tare da kashe sojoji biyar da dan sanda daya a Allawa.

An samu labarin cewa an kashe hudu daga cikin ‘yan bindigan a nan take yayin da aka ga gawarwakin mutum biyu a gona yayin da aka ce sun mutu ne sakamakon raunin harbin bindiga. Har yanzu rundunar ‘yan sandan Neja ba ta fitar da wata sanarwa game da lamarin ba.

Kiraye-kiraye da sako da aka aike wa jami’in hulda da jama’a na ’yan sandan Neja, DSP Wasiu Abiodun ba a amsa su ba a lokacin hada wannan rahoton.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here