Magidanci ya Mutu Bayan Shan Kwalaben Burkutu Guda 9 a Plateau

 

Wani magidanci a karamar hukumar Bokkos ta Jihar Plateau ya rasu bayan shan kwalaben burkutu guda 9 a Plateau.

Rahotanni sun bayyana cewa mutumin da ba a bayyana sunansa ba ya cika baki cewa zai iya shan kwalba 11 ba tare da ya bugu ba.

Amma bayan ya kwankwadi kwalabe tara cikin 11, ya gaza shanye sauran kuma ya fadi nan take yana fitar da jini daga baki da hanci da kunne.

Plateau – Wani mutum da ba a riga an gano sunansa ba a karamar hukumar Bokkos ta Jihar Plateau, wanda ya yi barazanar zai iya shan kwalabe tara na giyar gargazajiya (burkutu) ta tare da ya bugu ba ya mutu.

Hafsat Abubakar ta cibiyar shugabannin mata da sulhu ta Women Leaders of the Conflict Mediation Mitigation Regional Council (CMMRC) reshen jihar Plateau ta tabbatar da lamarin.

Ta ce mutumin da ba a gano sunansa ba ya bukaci mai sayar da burkutun ta bashi kwalabe 11 ya rantse zai iya shanye wa ba tare da ya bugu ba ko wani kunya ya faru.

Yadda lamarin ya faru Abubakar, wacce aka bawa labarin abin da ya faru a wurin shan burkutun, ta shaidawa The Nation cewa mutumin ya shanye kwalabe tara amma ya gaza shanye sauran biyun.

Nan take mutumin ya mutu yayin da mai sayar da burkutun ta tattara kayan ta ta tsere.

Kafin mutumin ya rasu, ya rika aman jini ta hancinsa da kunne da baki. Majiyar ta kara da cewa wani mafarauci, wanda ke wucewa ya ga gawar mutumin, ya sanar da mutanen kauyen su tafi su birne shi. An ce marigayin yana da matar aure daya da yara biyar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here