Jami’an Tsaro sun Kama Magidanci Kan Zargin yi wa ƴarsa Ciki a Bauchi

 

Rundunar ƴansandan jihar Bauchi ta kama wani mutum mai shekara 50, bisa zargin yi wa ƴarsa ciki a ƙauyen Kurmi Ado da ke ƙaramar hukumar Ganjuwa a jihar.

Kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Ahmed Wakil ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, inda ya ce rundunarsu na shirin gurfanar da shi a gaban kotu.

Rundunar ƴansanda ta ce tana zargin mutumin mai shekara 50 da cewa ya riƙa yi wa ƴar tasa mai shekara 17 fyaɗe, lamarin da ya sa har ta kai ga ɗaukar ciki.

SP Wakil ya ce bayan samun rahoton zargin ne rundunar a fara gudanar da bincike tare da kama mutumin.

Kakakin ƴansandan ya ce a lokacin da ake yi wa magidancin tambayoyi ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, inda kuma binciken likitoci ya tabbatar da cewa ya jima yana lalata da yarinyar, inda har take ɗauke da ciki.

SP Wakil ya ƙara da cewa a lokacin da ƴansanda ke yi wa yarinyar tambayoyi ta tabbatar da tuhumar mahaifin nata, tana mai cewa lamarin ya faru ne a lokacin da mahaifiyarta ta yi bulaguro zuwa wajen danginta.

A lokacin da mahaifiyar ta dawo ne ta fahimci ƴar tata na da ciki, inda bayan ta tuhumeta ta ce mahaifnta ne ya yi mata, kamar yadda ƴandandan suka bayyana.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here