Maguɗin Zaɓe da Tuggu Aka yi Min – Trump
Duk da ofishin shugaban kasa ya fara barinsa, har yanzu shugaba Donald Trump ya ki saduda cewa an kayar da shi a zabe.
Trump ya kekasa kasa, ya yi mirisisi, tare da yin tsaiwar gwamen jaki, a kan cewa shine ya lashe halastaccen zabe.
Tuni zababben shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya fara shirin shimfida salon mulkinsa da zarar an rantsar da shi a watan Janairu.
Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, a ranar Laraba, ya gayawa magoya bayansa cewa sai sun yi aiki tuƙuru don kawar da sakamakon zaɓen Amurka da ya bawa abokin hamayyarsa, Joe Biden, nasara.
Trump ya yi iƙirarin cewa an tafka “maguɗi” a zaɓen don tabbatar da ɗan takarar Democrat, Joe Biden ya samu galaba a kansa.
Read Also:
“Ya zama dole mu kawar da wannan zaɓen”, Trump ya fada a lokacin da ya kira magoya bayansa a Pennsylvania ta wayar tangaraho.
Fiye da sati uku kenan da Trump ya sha kayi a hannun Biden, ta hanyar bashi tazarar miliyoyin kuri’u, a wani salo da za’a iya bayyana wa da ‘kayen Allah tsine uwar mai ƙarya’.
“An tafka maguɗin zaɓe” a cewar Trump, inda ya yi ta kawo irin ƙulle-ƙulle da tuggun da aka shirya a wajen gudanar da zaɓuka a ƙasar.
Trump dai ya daɗe yana iƙirarin cewa an yi masa mamure tare da tafka maguɗi a zaɓen Amurka na bana, 2020, don ganin ya sha kayi, inda yace sam ba zai lamunci hakan ba.
Tun kafin a gudanar da zaben kasar Amurka, Legit.ng Hausa ta rawaito cewa motar yaƙin neman zaɓen Biden/Harris ta tsaya cak a kan hanya a Pflugerville, wani gari a Texas, sakamakon harin da gungun magoya bayan Trump suka kai mata.
Lamarin ya jawo an dakatar da gudanar da yakin neman zaben Biden a lokacin saboda dalilan tsaro.