Mahara Sun Kashe Mutane 12 a Zamfara
Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane fiye da 10 a Ƙaramar Hukumar Kauran Namoda ta Jahar Zamfara ranar Alhamis da dare.
Wani ɗan asalin yankin ya shaida wa BBC Hausa cewa maharan sun afka wa garin Sakajiki, inda suka ƙona motoci kusan bakwai ciki har da ta ‘yan sanda biyu.
Mutumin wanda muka ɓoye sunansa saboda dalilai na tsaro ya ce har yanzu bai yi magana da ‘yan uwansa ba da ke Ƙaura Namoda saboda katse layukan waya da aka yi.
Sai dai ya ce sun samu labari daga waɗanda suka samu fita daga garin zuwa Gusau babban birnin jahar cewa mutum 12 ne aka kashe tare da ƙona shaguna masu yawa.
Gwamnatin Zamfara a yankin arewa maso yammacin Najeriya ta katse layukan salula da zummar katse hanzarin ‘yan fashi da ke zaune a dazuka masu garkuwa da mutane. Daga baya an buɗe layukan a Gusau.
Su ma jahohin Neja da Kaduna da Katsina da ke yankin sun ɗauki irin wannan mataki.