Garkuwa da Ita: Mace Mai Ciki ta Haɗa Baki da Masu Garkuwa 

 

Wata Nafisa Saleh ta hada kai da mutane 2 wurin garkuwa da kan ta.

Lamarin ya faru ne a Damaturu, babban birnin jahar Yobe.

Tun ranar 1 ga watan Oktoban 2021 ta boye yayin zuwa asibiti yin awo.

Jahar Yobe -Wata mata mai suna Nafisa Saleh, mai ciki, ta hada kai da mutane 2 wurin garkuwa da kan ta a Damaturu, babban birnin jahar Yobe.

Kamar yadda Daily Trust ta rawaito, an neme ta an rasa ne tun ranar 1 ga watan Oktoban 2021 tana hanyar zuwa asibitin kwararru dake Damaturu don yin awo.

Bayan garkuwa da ita, wadanda su ka hada kai da ita sun kira mijin ta inda su ka bukaci ya biya kudin fansa.

Ta yi hakan ne don tatsar kudi wurin mijin ta da ‘yan uwan ta

Saidai binciken ‘yan sanda ya bayyana cewa daga baya aka gano cewa Nafisa da kanta ta sa aka yi garkuwa da ita don tatsar kudi a hannun mijin ta da ‘yan uwan ta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jahar Yobe, ASP Dungus Abdulkarim a wata takarda ta ranar Talata ya bayyana cewa ‘yan sanda sun yi gaggawar fara aikin su sannan su ka gano gaskiyar lamarin.

A cewar sa, rundunar ‘yan sanda ta kama mutane 2, Goni Modu da Umar Mai Gudusu duk ‘yan kauyen Dadinge dake karamar hukumar Gujba a jahar.

Saidai an yi gaggawar wucewa da Nafisa zuwa asibiti don duba lafiyar ta saboda halin da aka tsince ta a ciki.

Kamar yadda Daily Trust ta rawaito, Dungus ya kara da bayyana cewa sun kama wasu mutane 2 da ake zargin sun yi garkuwa da wani yaro mai shekaru 3 a karamar hukumar Potiskum dake jahar Yobe.

Masu garkuwa da mutanen duk yara ne kanana A cewar sa:

“Duk wadanda ake zargin yara ne, daya shekarun sa 14 dayan kuma 12, sai dai na ukun ya tsere.

“Idan ba a manta ba a ranar 18 ga watan Satumban 2021, an yi garkuwa da Adamu Abubakar Baban Yaro mai shekaru 3, sannan an sake shi bayan amsar N50,000 a matsayin kudin fansa.”

Ya kara bayyana yadda rundunar ta zage wurin bincike don kama duk wasu miyagun mutane a fadin jahar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here