Majalisar Dokoki ta Dakatar da Shugaban Karamar Hukuma a Jihar Legas

 

Jihar Legas – Majalisar dokokin jihar Legas ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Alimosho, Jelili Sulaimon, daga kan muƙaminsa.

A cewar ƴan majalisar, dakatarwar da aka yi wa shugaban ƙaramar hukumar za ta fara aiki ne nan take ba tare da ɓata wani lokaci ba.

Majalisa ta dakatar da ciyaman

Jaridar Tribune ta rahoto cewa ƴan majalisar dokokin sun dakatar da Jelili Sulaiman ne a yayin zamansu na ranar Litinin, 7 ga watan Oktoban 2024.

A zaman da suka yi na ranar Litinin, ƴan majalisar sun yanke shawarar cewa mataimakin shugaban ƙaramar hukumar, Mista Akinpelu Johnson, ya karɓi ragamar tafiyar da harkokinta, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Majalisar ta kuma umarci mahukuntan ƙaramar hukumar da suka haɗa da manaja da ma’aji da su amince da ikon mataimakin shugaban tare da ba shi dukkanin goyon baya domin ya gudanar da aikinsa yadda ya kamata.

Meyasa aka dakatar da shi

Ƴan majalisar dai sun dakatar da Sulaiman Jelili ne daga muƙaminsa bayan sun kaɗa ƙuri’ar amincewa ta bai ɗaya kan ƙudirin neman a dakatar da shi.

Ana dai zarginsa ne da rashin bin dokoki, bijirewa da rashin biyayya ga majalisar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here