Majalisar Wakilan Najeriya ta Gayyaci Gwamnan CBN da Shugaban NNPC

Batun batan makudan kudade daga asusun gwamnati Najeriya da karkatar da kudaden haraji ba bakon abu bane.

A wannan karon, majalisar wakilai ta ce tiriliyan uku da biliyan ashirin da hudun sun yi batan dabo, ba a san yadda aka yi da su ba.

Majalisar ta ce ya zama wajibi gwamnan CBN da shugaban NNPC su bayyana a gabanta domin yin bayani a kan makomar kudade.

Majalisar wakilan Najeriya ta aika takardar gayyata zuwa ga shugaban kamfanin mai na kasa (NNPC) da kuma gwamnan babban bankin kasa (CBN) domin su yi bayani a kan batan dabon wasu kudade masu nauyin gaske.

A cewar majalisar, Naira tiriliyan uku da biliyan ashirin da hudu sun bata daga cikin kudaden cinikayyar man fetur a shekarar 2014.

Dan majalisa, Wole Oke, mai shugabantar kwamitin kula da asusun gwamnatin tarayya ya ce bayanai daga ofishin babban mai binciken kudi na tarraya ne suka nuna hakan.

Honarabul Oke ya ce bayan kwamitinsa ya samu bayanai da shaidun batan kudin, ya aika takardar tuhuma zuwa NNPC da CBN.

Kwamitin ya ce akwai bukatar shugaban NNPC, Malam Mele Kyari, da gwamnan CBN, Godwin Emefiele, su bayar da bayani a kan batan kudaden. Duk da kwamitin ya koka a kan cewa Kyari ya ki amsa gayyatar da aka taba yi masa a baya, ya ce ya zama farilla yanzu ya amsa gayyata domin sanar da yadda aka yi da kudaden.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here