Cire Takunkumin ba da Dala: Majalisar Wakilai ta Gayyaci Gwamnan CBN

 

Yayin da gwamnan CBN, Yemi Cardoso ya dauki matakin soke samar da dala ga wasu kayayyaki, Majalisar Wakilai ta nemi bahasi.

Majalisar ta ce dole Cardoso ya zo gabanta don fayyace musu komai kan wannan mataki da ya dauka da ake ta cece-kuce a kasar.

Mutane da dama na hasashen wannan mataki da bankin CBN ya dauka zai saukar da kayayyaki musamman na abinci da sauransu.

FCT, Abuja – Majalisar Wakilai ta umarci gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN ya hallara a gabanta don yi bayani kan matakin soke tsarin ba da dala kan kayayyaki 43.

Gwamnan CBN, Yemi Cardoso ya dauki matakin soke ba da dalar ce ga wadansu kayayyaki 43 don inganta tattalin arzikin kasar, cewar TheCable.

Meye ya jawo gayyatar da majalisar ta yi wa gwamnan CBN?

Wannan na zuwa ne bayan jama’a na ta hasashen cewa hakan zai karya farashin kayayyaki ganin yadda dalar ke taimakawa wurin kara farashin kaya a kasar.

Mambobin majalisar sun tabbatar da haka ne a yau Talata 24 a watan Oktoba yayin zaman majalisar a Abuja.

Wannan ya biyo bayan kuduri da mamban majalisar, Sada Soli daga jihar Katsina ya gabatar a gaban majalisar.

Meye ake hasashen matakin na CBN zai jawo?

Yayin gabatar da kudirin, Soli ya ce hakan wannan mataki na iya tilasta rufe masana’antu da kuma kawo matsala a harkokin tattalin arziki.

Ana shi martanin, Jesse Onuakalusi, mamba mai wakiltar Oshodi/Isolo II da ke jihar Legas ya ce dole bankin ya dakatar da wannan mataki har sai majalisa ta gama bincike.

Masana sun yi bayani kan cire takunkumin CBN A wani labarin, a kwanakin baya. Bankin CBN, ya cire takunkumi wajen ba da dala domin shigo da wasu kayayyaki 43 zuwa kasar.

Mutane da dama na hasashen hakan zai rage tashin farashin kaya ganin yadda dalar ke kara hauwawar farashin kaya musamman abinci.

Sai dai wasu masana sun yi bayani cewa hakan ba ya na nufin dole abinci zai yi tsada a kasar ba ne kamar yadda ake hasashe.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com