Majalisar Dokokin jahar Plateau ta Magantu Kan Matsalar Rashin Tsaro a Jahar

 

Majalisar dokokin jahar Filato ta yi Allah wadai da kashe-kashen da ke faruwa a garuruwa daban-daban a Jos.

Wasu mazauna jahar ba su ji dadin yadda gwamna Simon Lalong ya tafiyar da lamarin ba.

‘Yan majalisa a Filato sun yi kira ga Lalong da ya fito da kwararan matakai kan yadda za a dakatar da kalubalen tsaro a jahar.

Rahotannin da ke fitowa sun nuna cewa ‘yan majalisar dokokin Filato na fuskantar matsin lamba na tsige gwamna Simon Lalong kan karuwar hare -hare a jahar.

An dora alhakin rikicin jahar kan karo tsakanin ‘yan asalin yankin da Fulani mazauna yankin.

Jaridar Tribune ta rawaito cewa mazauna jahar da suke ganin Gwamna Lalong yana da ra’ayin Fulani ne ke neman a dauki mataki akan gwamnan.

Rahoton ya bayyana cewa wasu daga cikin ‘yan majalisar sun tabbatar da cewa suna fuskantar matsin lamba daga ‘yan mazabarsu da suka zarge su da hadewa da gwamnan don yin watsi da su cikin rashin tsaro.

Wani dan majalisar da baya son a ambaci sunansa ya bayyana cewa har yanzu majalisar bata yanke shawara kan ko za a fara sharin tsige gwamnan ba ko a’a.

Ya ce majalisar za ta yanke hukunci idan gwamnan ya gaza magance matsalolin tsaro da ke damun jahar cikin makwanni biyu.

Jaridar The Guardian ta rawaito cewa Philip Dasun, shugaban kwamitin majalisar kan bayanai ya shaidawa manema labarai a Jos cewa yan majalisan sun himmatu wajen tabbatar da dawowar zaman lafiya a jahar.

Ya ce:

“A matsayin mu na majalisa da ke dauke da mutane a zucciyarmu, muna kira ga ‘yan Filato da su kasance masu dogaro da mu.

“Mun bai wa gwamnan makonni biyu ya dauki mataki kan kudurorin da majalisar ta gabatar kan harkokin tsaro da yadda za a maido da zaman lafiya.

“Muna kira ga Gov. Simon Bako Lalong ya fito da wata sanarwa da za ta kare mu a matsayin mu na al’umma da kuma dawo da sabon sadaukar da kai ga aikin Filato.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here