NERC ta Umarci Kamfanonin Raba Wutar Lantarki da su Kara Farashin Wutar

 

Gwamnatin tarayya ta amince da kara farashin wutar lantarki daga Satumba.

Wannan ya biyo karin da akayi a 2020 ta ninki biyu.

Tuni wasu kamfanonin raba wuta sun fara sanar da kwastamominsu.

Lagos – Hukumar lura da wutar lantarkin Najeriya (NERC) ta umurci kamfanonin raba wutar lantarki 11 (Discos) su kara farashin wuta fari daga ranar 1 ga watan Satumba, 2021.

Bisa wani takarda da jaridar TheNation tayi ikirarin gani yau, hukumar NERC ta baiwa kamfanonin damar kara kudin ne a wasikar mai taken “Sanarwan Karin Farashi.”

Hakazalika an tattaro cewa a wani takarda mai lamba ”023/EKEDP/GMCLR/0025/2021, kamfanin raba lantarkin Eko (EKEDC), ya sanar da kwastamominsa cewa za’a yi karin kudin wuta daga ranar 1 ga Satumba, 2021.

Eko Disco ya sanar da kwastamominsa cewa:

“wannan kari zai bayyana a kan takardar biyan kudin wuta na Oktoba 2021, wanda ke nuna adadin wutan da akayi amfani da shi a watan Satumba.”

“Amma kwastamomi masu amfani da mita, muna kira gareku ku gyara mitocin zuwa sabon farashin da NERC tayi umurni.”

Yayinda aka tuntubi mai magana da yawun hukumar NERC, bai daga wayarsa ba kuma bai amsa tambayar da akayi masa ta sakon akwatin SMS ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here