An Samun Nasarori Masu Yawa a Yaki da Ta’addanci a Fadin Kasar nan – Garba Shehu

 

Fadar shugaban kasa ta magantu kan kokarin da gwamnati mai ci ke yi wajen yaki da masu tayar da kayar baya da fashi da makami a kasar.

Malam Garba Shehu ya ce “ana samun nasarori masu yawa” a yaki da ta’addanci a fadin kasar.

Da yake zantawa da BBC Pidgin a ranar Asabar, Shehu ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa ‘yan fashi abu mafi muni fiye da tunanin kowa.

Abuja – Garba Shehu, hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, ya bayyana cewa ana samun “manyan nasarori” a cikin yaki da gwamnatin tarayya ke yi da ‘yan fashi da masu ta’addanci.

Shehu ya bayyana hakan ne da safiyar Asabar, 28 ga watan Agusta, yayin wata hira da BBC Pidgin wanda Legit.ng ta sanya ido.

A cewarsa, an yi watsi da nasarorin da aka samu a yaki da ta’addanci, fashi da makami da sauran laifuka.

Ya kara da cewa an kara himma don tabbatar da cewa sojojin Najeriya sun sami nasara cikin sauri kan masu kera muggan makamai.

Buhari ya muzanta wa ‘yan fashi

Da yake tabbatar da kokarin da gwamnati mai ci a yanzu ke yi na yaki da miyagun laifuka da ta’addanci, Garba Shehu ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari “ta yi wa ‘yan bindigar da ke dauke da makamai abun da ya fi ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda muni.”

Hadimin shugaban kasar ya ce umurnin da Buhari ya bayar na harbe ‘yan bindigar da aka gani da AK-47 bai kai kan kungiyar da aka haramta na Indigenous People of Biafra (IPOB) ba.

Shehu ya ce ba a yiwa ‘yan bindiga rikon sakainar kashi ba-dalilin kenan da yasa sojojin Najeriya ke tayar da bama-bamai a wurarensu, sannan sojojin kasa na musayar wuta da su.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here