Majalisar Tarayya: Babu Wani Kayan Tallafin Korona da Muka Samu Daga Hannun Buhari

Majalisar tarayya ta wanke kanta daga zargin da jama’a suke yi mata.

Ta ce Shugaba Buhari bai ba ta kayan tallafin COVID-19 ba.

Ta ce babu kwabo ko tiyar shinkafa da shugaban kasa ya bata Majalisar tarayya, kwamitin kungiyar yakin neman zaben Buhari na 2019, ta musanta zargin adana kayan tallafin COVID-19 da aka bada don raba wa ‘yan Najeriya.

A cewar majalisar, babu wani sanata da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bai wa kudi ko kuma kayan tallafin COVID-19, Vanguard ta wallafa.

Sun gode wa shugaban kwamitin yada labarai da kamfen din Buhari, Engr. Kailani Muhammad, da yayi gaggawar sanar da su abinda ake ciki, inda suka ce babu wani dan majalisa da aka bai wa kayan tallafin.

A cewar majalisar, ko tiyar shinkafa basu gani ba, sannan ko sisi ba a raba mu su ba, balle su adana.

Kamar yadda majalisar ta saki wata takarda a ranar Litinin a Abuja, wacce shugaban kwamitin yada labarai, Sanata Ajibola Basiru ya saka hannu, sun ce a daina shafa musu kashin kaji.

A cewar majalisar, ba rabin albashinsu kadai su ka bayar ba, har raba wa mutane kayan tallafi suka yi daga aljihunsu, duk don taimakon wadanda suka yi laushi lokacin da ake ganiyar annobar COVID-19.

Majalisar ta kara da cewa, ba su ga dalilin da zai sa Kilani Mohammed ko kuma wani ya zargesu da wannan laifin ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here