Majalisar Dattawa ta Matsa Akan Sai an cire Shugabanin Tsaro

Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sallami hafsoshin tsaro da suka dade kan mulki.

Yan majalisan sun yanke wannan shawara na aikewa Buhari sakon ne sakamakon kudirin da Sanata mai wakiltar Borno ta tsakiya, Kashim Shettima, ya gabatar gaban majalisa.

Wannan bukata ya zo watanni shida bayan majalisar ta bukaci hafsoshin tsaro suyi murabus daga kujerunsa saboda sun gaza.

Hafsoshin tsaron da ya kamata a ce tuni sun yi ritaya amma shugaba Buhari ke cigaba da amfani sune shugabansu, Janar Gabriel Olonisakin; shugaban sojin kasa, Laftanan Janar Tukur Buratai; Shugaban Mayakan Sama, Air Marshal Sadique Abubakar da shugaba Sojin ruwa, Ibok-Ete Ekwe Ibas.

Shettima ya janyo hankalin Sanatocin ne zuwa kisan manoma 45 da aka yi a kauyen Kwashabe, wani gari dake da nisan kilomita 20 da birnin jihar Borno, Maiduguri.

A karshen zaman majalisa na ranar Talata, 1 ga watan Disamba, yan majalisan sun yi ittifakin cewa:

“Majalisa na kira ga gwamnatin tarayya tayi gaggawan shirye-shiryen cire hafsoshin tsaro da suka wuce wa’adinsu, kuma a mayesu da sabbi masu sabbin tunani da mafita.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here