Majalisar Dattijai ta Amince da Haliru Nababa a Matsayin Shugaban Hukumar Gyaran Hali
Majalisar dattijai ta amince da bukatar shugaba Muhammadu Buhari na nadin shugaban hukumar dake kula da gidan gyaran hali wato kurkuku.
Majalisar ta amince da nadin ne biyo bayan sauraron rahoton da kwamitin ta ya bayyana a zaman ta na yau Laraba.
Shugaban Kwamitin sanata Kashim Shettima na jam’iyyar APC ne ya bayyana rahoton inda yace Nababa ya cancanci ya rike ofis din
A ranar Laraban nan majalisar dattijai ta amince da naɗin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya turo mata na shugaban hukumar gyaran hali masu kula da kurkuku. Majalisar ta amince da Haliru Nababa a matsayin shugaban hukumar gyara hali wato (Correctional Service).
Amincewa da naɗin ya biyo bayan dubawa da kuma yarda da rahoton da kwamitin kula da ayyukan cikin gida na majalisar ya gabatar, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Read Also:
Lokacin da yake gabatar da rahoton, shugaban kwamitin, Sanata Kashin Shetima, na jam’iyyar APC daga jihar Borno yace babu wani rahoto na ƙara ko wani laifi da wanda akeson naɗawa yayi.
Ya kuma ƙara da cewa Haliru Nababa ya nuna matuƙar ƙwarewa da bayyana ya cancanta da ya riƙe wannan ofis ɗin.
Shetima yace Nababa ya cika sharuɗɗan sashi na 3 (2) na kundin tsarin hukumar gyaran hali ta ƙasar nan.
Shugaban kwamitin ya ƙara da cewa: “Wanda ake son naɗawa ya bayyana a gaban kwamitin mu domin tantancewa, ya kuma bayyana cewa rashin isassun makamai domin hana karya magarƙama, rashin isassun kuɗi, rashin yin kasafi me kyau a hukumar, da kuma rashin tsaruka masu kyau a hukumar sune manyan kalubalen da suka dabai-baye hukumar.”
Shettima ya ƙara da cewa: “Nababa ya kuma bayyana cewa cinkoson masu laifi a kurkuku na daga cikin abinda zai tasa a gaba idan ya shiga ofis, yace zai iya bakin kokarin sa wajen samar da wurare a kurkukun ƙasar nan, zamu haɗa hannu da masu ruwa da tsaki da gwamnoni wajen cimma manufar mu.”